Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan ‘yan Arewa a yankin Uromi, da ke Jihar Edo, inda ya umarci hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata laifin.
“Ba za a bari miyagu su ci gaba da zubar da jinin ‘yan Nijeriya ba tare da hukunta su ba. Dole ne a yi adalci,” cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar.
- Ribas: Ƙungiyar Ƙwadago Na Barazanar Shiga Yajin Aiki In Har Ba A Janye Dokar Ta-ɓaci Ba
- Gwamnatin Edo Za Ta Binciki Kisan Matafiya ‘Yan Arewa A Jihar
Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan sa-kai ne suka kashe matafiyan waɗanda da yawasu ‘yan asalin Jihar Kano ne.
Tinubu, ya nuna matuƙar takaicinsa kan lamarin, inda ya ce ɗaukar doka da hannu ba shi da gurbi a Nijeriya.
“Kowane ɗan Nijeriya na da ‘yancin tafiya ba tare da fargabar hari ba,” in ji shi, yana tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare lafiyar al’umma.
Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, da shugabannin al’ummar Uromi bisa matakin da suka ɗauka domin daƙile yiwuwar tashin hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp