Shugaba Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya É—auki matakai don karya farashin abinci a faÉ—in Nijeriya.
Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana ɗaya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba.
- Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
- Shettima Ya Yaba Wa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Ƙwarewa Ta Jihar Kaduna
Ya ce shirin rage farashin abinci ya haɗa da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauƙi.
Sanata Abdullahi ya ƙara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni.
Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauƙi, wanda zai taimaka wajen rage farashin abinci.
Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa.
Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp