Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya warware takaddamar filaye da ke tsakanin jami’ar Bayero Kano da kauyen da ke makwabtaka da ita – Rimin Zakara, ta hanyar mayar da filin ga jami’ar.
Tinubu ya bukaci hakan ne a ranar Asabar a Kano yayin bikin taron yaye Dalibai karo na 39 na Jami’ar Bayero, inda Shugaban kasar ya samu wakilcin karamar ministar ilimi, Suwaiba Ahmed.
- Mummunan Hatsari Ya Kashe Mutane 23, Da Yawa Sun Jikkata A Kano
- Wang Yi: Ya Kamata A Daukaka Tsarin Tafiyar Da Dokokin Duniya Karkashin Jagorancin MDD
Shugaban ya yi kira ga gwamnan da ya dauki matakin gaggawa ta hanyar bayar da takardar shaidar mallakar filaye ga jami’ar don warware matsalar, inda ya jaddada mahimmancin filayen ga jami’ar.
Bugu da kari, Tinubu ya amince da rashin shinge a sabuwar harabar jami’ar ne ya kawo wannan takaddamar, inda nan take ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta ware kudade domin gudanar da aikin kafa katafaren shinge a tsakanin kauyen da Jami’ar.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin na inganta ababen more rayuwa na jami’o’i a fadin kasar nan.