Shugaba Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ayarin dubban mutanen da suka bude shafi a sabuwar manhajar Threads kishiyar Twitter.
Mashahurin Mai kudin nan kuma mamallakin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, ne ya ƙaddamar da Zaren don yin gasa da Elon Musk mai kamfanin Twitter.
- Tinubu Zai Sanar Da Sabuwar Ranar Kidayar Jama’a Da Gidaje – NPC
- Tinubu Ya Yi Garambawul Kan Dokokin Haraji
Meta ya ce sama da mutane miliyan 30 ne suka yi rajistar bude sabon shafin na Threads zuwa wannan lokaci.
Shugaba Tinubu ya wallafa rubutunsa na farko kan Threads kamar sauran mabiya sabuwar manhajar.
Fitattun ‘yan Nijeriya, wadanda suka yi rajistar a manhajar sun hada da mawaka da ‘Yar fim da dai sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp