Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya dora wa sabbin ministoci aiki da su cika burin ‘yan Nijeriya na samun wani sabon ci gaba ta fudkar tattalin arziki.
Shugaban ya bayyana haka ne bayan rantsar da ministocin a dakin taro na Banquet da ke fadar gwamnati a ranar Litinin a Abuja.
- NNPP Ta Maka Kwankwaso A Kotu Kan Zargin Yi Wa Jam’iyya Makarkashiya
- Atiku, Kwankwaso Da Obi Sun Fara Tattaunawa Kan Samar Da Babbar Jam’iyyar Hamayya Daya Tilo
Ya ce gwamnatin ta zo a daidai lokacin da kasar ke bukatar gyara ta kowane fanni.
“Yan Nijeriya suna sa ran za ku taka muhimmiyar rawa kamar yadda muka alkawarta musu a lokacin yakin neman zabe. Daga rantsar da ku a yau, kun zama ministocin Tarayyar Nijeriya ba ministocin wata jiha ko yanki ba.
“‘Yan Nijeriya suna tsammanin ganin abubuwa da kuma sun cancanci son ganin canje-canje a rayuwarsu. Yanzu kuna cikin jirgin ruwa ɗaya tare da ni kuma suna tsammanin rayuwarsu za ta ɗauki sabon salo mai kyau, ”in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp