Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan wata ziyarar aiki ta kwanaki biyar da ya kai birnin Berlin na kasar Jamus, inda ya halarci taron G20 Compact.
Yayin da ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 8 na daren Laraba, shugaban ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da jam’iyyar APC mai mulki da suka hada da ministan babban birnin tarayya, Cif Nyesom Wike, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
- Mun Ciwo Bashin Biliyan 100 Don Gudanar Da Ayyukan More Rayuwa – Gwamnan Bauchi
- Gwamna Nasir Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 250 Ga Majalisar Dokokin Kebbi
A lokacin ziyarar, Shugaba Tinubu ya da hada kai da sauran shugabannin kasashe da gwamnatoci don bunkasa ci gaban tattalin arziki da kasuwanci a Afrika.
Taron na G20 shi ne karo na hudu, wanda gwamnatin Jamus da kungiyoyin ‘yan kasuwa suka shirya.
A ci gaba da karfafa alakar diflomasiyya, shugaban ya tattauna da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz da wasu manyan jami’ai a ranar Litinin.