Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasar Brazil domin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Jirgin shugaban ƙasar ya tashi daga filin jirgin saman Brasília International da ƙarfe 12:57 na rana agogon ƙasar.
- Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya
- Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa jami’an Brazil, Jakada Carlos Sérgio Sobral Duarte da Jakada Carlos José Areias Moreno Garcete tare da Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da wasu jami’an gwamnati, sun raka shi zuws filin jirgin.
An gudanar da ƙaramin bikin bankwana tare da girmamawar dakarun soja ƙarƙashin jagorancin Col. Cel Nicolas.
Tinubu ya isa birnin Brasília ne a ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, inda aka tarbe shi a Fadar Shugaban Kasa, Palácio do Planalto.
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar.
Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya.