Ana ci gaba da rade-radin cewar Shugaba Bola Tinubu zai sauke wasu ministocinsa da ba su yi abun a zo a gani ba.
Wannan na zuwa ne bayan zaman majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) da Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
- Tsohuwa Ta Yi Barazanar Kai Ƙarar Wanda Ya Shirya Gasar Cin Taliya Da Jikanta Ya Lashe
- Kafa Karamin Rukuni Domin Mayar Da Wani Sashe Saniyar Ware Ba Zai Haifar Da Da Mai Ido Ba
Rahotanni da dama sun nuna cewa Tinubu na shirin yin wasu sauye-sauye nan ba da jimawa ba, bayan ya yi barazanar sallamar wasu ministocinsa da ba su taka rawar gani ba.
Duk da haka, shugaban bai tabbatar da takamaiman lokaci ko yadda sauyin zai gudana ba.
A taron majalisar, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya jinjina wa Tinubu kan rawar da ya taka wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Jihar Edo.
Ya kuma taya jam’iyyar APC, murna kan nasarar da suka samu a zaɓen Sanata da aka gudanar kwanan nan a jihar.
Akume, ya kuma sanar da majalisar game da rasuwar tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Salome Jankada, wadda ta rasu a ranar 27 ga watan Agusta.
Majalisar ta yi ta’aziyya tare da girmamawa ga tsohuwar ministar.
Manyan jami’an gwamnati irin su Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu ministoci sun halarci taron.
Sai dai hankali ya karkata kan yiwuwar Tinubu na sauya ministocinsa a nan gaba kaÉ—an.