Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa ƙasar Japan a wani muhimmin ziyarar aikin ƙasa da ƙasa domin halartar taron Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) karo na tara.
Shugaba Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Haneda, Tokyo, da misalin ƙarfe 12:55 na safe agogon ƙasar Japan a ranar Talata, inda Jakadan TICAD, Hideo Matsubara, ya tarɓe shi. Wannan shi ne karo na farko da Shugaban Nijeriyar zai kai ziyara ta aiki a Japan tun bayan hawansa karagar mulki watanni 25 da suka gabata.
- Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda
- Fim Na Kisan Kiyashin Da Sojojin Japan Suka Yi A Birnin Nanjing Na Samun Karbuwa A Kasar Sin
A birnin Yokohama, Tinubu zai yi amfani da taron wajen gabatar da Nijeriya a matsayin cibiyar zuba jari ga ƴan kasuwar Japan, musamman waɗanda suke da harkoki a Nijeriya da kuma masu sha’awar shiga kasuwanci a fannoni daban-daban. Haka kuma zai halarci zaman taruka, ya gana da shugabannin ƙasashe da manyan ƴan kasuwa daga Japan.
Taron na bana, mai taken “Co-create Innovative Solutions with Africa,” na nufin ƙarfafa haɗin kai tsakanin Afirka da Japan, tare da samar da mafita ta hanyar sabbin fasahohi da ingantattun shirye-shirye. TICAD na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ci gaba mai ɗorewa, da haɓaka jarin fannoni masu zaman kansu da kuma gina muhimman cibiyoyi a nahiyar Afrika.
Tun daga kafuwarsa a 1993, TICAD ke zama babban dandalin tattaunawa tsakanin Japan da Afrika, wanda ake gudanarwa duk bayan shekaru uku, a Japan ko a wata ƙasa ta Afrika. Taron da ya gabata an gudanar da shi ne a Tunisia a 2022, yayin da wannan karo na 2025 ke gudana daga 20 zuwa 22 ga watan Agusta, inda shugabannin Afrika, da abokan cigaba, da ƴan kasuwa da ƙungiyoyin fararen hula ke halarta domin samar da hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi da ɗorewar zaman lafiya a nahiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp