Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya is Jihar Katsina domin tabar gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin London yana da shekaru 82.
Jirgin Shugaba Tinubu ya sauka a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina da misalin ƙarfe 1:45 na ranar Talata.
- Buhari Na Cikin Ƙoshin Lafiya Kwana Ɗaya Kafin Rasuwarsa – Mamman Daura
- Trump Ya Bai Wa Rasha Kwanaki 50 Ta Kawo Ƙarshen Yaƙinta Da Ukraine
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, tare da wasu gwamnoni, jami’an gwamnati, sarakuna da jami’an tsaro ne suka tarbe shi.
Zuwan Tinubu na cikin shirye-shiryen jana’izar Buhari.
Ana sa ran za a binne gawar Buhari a garinsu da le Daura, a Jihar Katsina.
Tun da farko, matar Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta isa Katsina domin halartar jana’izar.
Ta gana da ‘yan uwan Buhari, manyan baƙi, da masu zaman makoki da suka taru.
An tsaurara tsaro a Katsina da Daura yayin da dubban mutane ciki har da shugabannin siyasa, sarakuna, da jama’a suka fito domin yin bankwana da Buhari.
Buhari, ya shugabanci Nijeriya a matsayin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan a matsayin shugaban ƙasa na dimokuraɗiyya daga 2015 zuwa 2023.
An san shi da ƙwazo, yaƙi da cin hanci, da ƙoƙari wajen inganta tsaro.
Shugaba Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin “ɗan ƙasa na gari, soja kuma dattijo da ya sadaukar da rayuwarsa wajen haɗa kan Nijeriya da kawo ci gaba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp