Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa gwamnatin kasar Canada, jami’an diflomasiyya, da duk mutanen da gobarar ta shafa a ranar Litinin a babban ofishin jakadancin Canada da ke Abuja.
Shugaban a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya tabbatar wa hukumomin kasar Canada cikakken goyon bayan gwamnatin Nijeriya wajen taimakon jami’an diflomasiyya da na cikin gida na babbar hukumar da lamarin ya shafa.
- Tinubu Zai Halarci Tarukan Kasashen Afrika Da Larabawa A Kasar Saudiyya
- Ku Yi Aiki Tukuru Ko Na Kore Ku, Tinubu Ga Ministoci
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu tare da yi wa duk wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, akalla mutane biyu ne ake fargabar sun mutu, daya kuma ya samu munanan raunuka sakamakon gobarar da ta tashi a wani bangare na ofishin jakadancin Canada da ke Abuja a ranar Litinin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp