Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci janye nadin Injiya Ibrahim Kashim Imam a matsayin shugaban hukumar kula da lafiyar hanyoyi gami da musu kwaskwarima wato (FERMA).
A cewar wata sanarwa da kakakin shugaban kasan, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya janye nadin dan shekara 24 din ne nan take ba tare da bata lokaci ba.
- Motar Gidan Yari Ta Afka Kan ‘Yan Kasuwa A Kwara
- Wasu Kauyukan Sin Sun Shiga Jerin Mafiya Kayatarwa A Fannin Yawon Bude Ido
“Dukkanin sauran nade-naden da aka yi wa majalisa da hukumar gudanarwar FERMA ba su shafi wannan umarnin ba,” a cewar sanarwar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa nadin da Tinubun ya yi wa Imam tare da sauran mambobin hukumar gudanarwar FERMA an bayyana ne a makon jiya, wanda hakan ya janyo suka da muhawara a tsakanin ‘yan kasa.