ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

by Abubakar Abba
7 months ago
Tinubu

Sashen samar da wadataccen abinci da ke karkashin kulawar Fadar Shugaban Kasa (PFSCU), a kwanan baya ne ya hada wani taron tattaunawa da manyan kafafen yada labarai da kuma ‘yan jarida, masu dauko rahotannin aikin noma na kasar nan.

An gudanar da tattaunawar ce a birnin tarayyar Abuja, da nufin hada karfi da karfe; domin kafafen yada labaran da kuma ‘yan jaridar da ke dauko labaran aikin noma, su bayar da goyon bayansu wajen yada rahotannin aikin samar da wadataccen abinci a kasar.

  • Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

A taron, an tattauna kan gudunmawar da kafafaen yada labaran za su bayar, musamman wajen wayar da kan ‘yan Nijeriya kan burin samar da wadatacen abinci a fadin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Marion Moon, mai taimakawa shuagaban kasa a bangaren aikin noma da kuma sashen na PFSCU, ya jadda muhimmancin kara mayar da hankali da gwamnatin mai ci ke kan yi, na kara habaka fannin aikin noma a kasar, musamman ta hanyar samar da trsare-tsare da kuma dabaru.

Ya sanar da cewa, ya zama wajibi Nijeriya ta cimma burin da ta sanya a gaba na samar da wadataccen abinci a kasar, inda ya kara cewa; hakan ne yasa aka jawo kafafen yada labaran, domin cimma wannan buri.

LABARAI MASU NASABA

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma.

Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar ke yi, wajen bayar da tallace-tallacen da suka shafi bangaren aikin noma, inda suka yi nuni da cewa, kafafen yada labarai; sun dogara ne kacokan a kan samun tallace-tallace, wanda akasari shi ne ke rike da su.

Sun kuma bukaci a samar wa da kafafen yada labaran kasar, wata hanyar sadarwa ta bai daya, musamman domin su kara wallafa rahotannin da suka shafi ayyukan gwamnatin kasar na aikin noma.

Mahalarta taron, sun kuma amince da kara daga matsayin aikin noma na kasar, ciki har da bai wa ‘yan jarida horo a kai-kai kan abin da ya shafi wallafa rahotannin aikin noma.

Sahen na PFSCU, ya mayar da hankali ne wajen ganin yin hadaka da cibiyoyi, musamman domin gwamnatin tarayya ta cimma burin samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kara habaka fannin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abubuwa Biyar Game Da Kiwon Talotalo
Noma Da Kiwo

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

December 20, 2025
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa
Noma Da Kiwo

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

December 19, 2025
Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman
Noma Da Kiwo

Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman

December 14, 2025
Next Post
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.