Shugaba Bola Tinubu, ya sauke Mele Kyari daga muƙaminsa na Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), tare da rushe kwamitin gudanarwarsa, daga ranar 2 ga watan Afrilu, 2025.
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasa ne ya sanar da hakan, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin inganta aiki da bunƙasa NNPC a matsayin kamfani mai zaman kansa.
- Duk Da Hanin Gwamna Da ‘Yansanda, Natasha Ta Isa Gida Kuma Ta Yi Taro
- Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi
An naɗa Bayo Ojulari a matsayin sabon Shugaban Kamfanin, wanda zai maye gurbin Kyari, yayin da Ahmadu Musa Kida ya zama sabon Shugaban Kwamitin Gudanarwa.
Haka kuma, an naɗa Adedapo Segun a matsayin Babban Jami’in Kuɗi.
An kuma naɗa wasu shuwagabanni guda shida da ke wakiltar yankunan Nijeriya daban-daban, tare da wakilai biyu daga ma’aikatun Kuɗi da Albarkatun Man Fetur.
Gwamnatin Tinubu na da burin jan hankalin masu zuba jari da kuɗi har dala biliyan 30 nan da 2027 da kuma dala biliyan 60 nan da 2030.
Hakazalika, tana shirin ƙara yawan haƙar ɗanyen mai zuwa ganga miliyan uku a kowace rana nan da 2030, tare da ƙara yawan samar da gas zuwa biliyan goma a kowace rana.
Shugaban ƙasa ya buƙaci sabbkn shugabancin NNPC da su ƙara ƙarfin tace mai a gida don rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje da kuma ƙarfafa tsaron makamashi a Nijeriya.
Kida, sabon Shugaban Kwamitin Gudanarwa, da Ojulari, sabon Shugaban Kamfanin, dukkaninsu ƙwararru ne a harkar man fetur.
Tinubu ya gode wa shugabannin da aka sauke bisa gudunmawar da suka bayar, musamman wajen farfaɗo da matatun mai na Fatakwal da Warri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp