Kamar yadda aka ruwaito a shafin farko na jaridar LEADERSHIP ta ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da rusa shugabannin gudanarwar hukumomin gwamnatin tarayya da na ma’aikatu da cibiyoyi da kuma kamfanonin gwamnati masu zaman kansu cikin gaggawa.
A cewar sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Willy Bassey, ya fitar da yammacin ranar Litinin.
- Da Dumi-Duminsa: Tinubu Ya Kori Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Ya Nada Sabbi
- DSS Ta Gano Shirin Da Wasu Ke Yi Na Bata Sunan Gwamnatin Tinubu Kan Cafke Emefiele
Sanarwar ta ce Jami’in da aka dakatar da su mika ragamar aikinsu ga manyan sakatarorin Ma’aikatun don sanya ido da gudanarwa da Hukumomi, Cibiyoyi, da Kamfanonin Gwamnati zuwa lokacin da Shugaban kasa zai nada wasu.
“An umurci manyan sakatarorin hukumomi da su aike da bayanai zuwa ga shugaban kasa ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
“Saboda haka, dukkan ma’aikatu, ma’aikatu da hukumomi su tabbatar da bin wannan umarni da ya fara aiki daga ranar Juma’a 16 ga watan Yuni, 2023.
“An umurci manyan sakatarorin dindindin da su sanar da shugabannin hukumomin da abin ya shafa a karkashin kulawar ma’aikatu/Ofisoshinsu domin a bi su cikin gaggawa,” in ji sanarwar.