Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa gobarar da ta yi sanadin mutuwar wasu masallata a wani masallaci da ke Larabar Abasawa a karamar hukumar Gezawa a jihar.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, ya yi Allah wadai da harin, ya kuma umurci jami’an tsaro da su tabbatar da gudanar da bincike mai zurfi tare da hukunta wanda ake tuhuma.
- Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yi Wa Dokar Da Ta Tsige Sarki Sanusi II Kwaskwarima
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 9, Sun Kwato Makamai A Kaduna
Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan mamatan, da duk wadanda abin ya shafa, ya kuma yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne wani Shafi’u Abubakar ya kona wani masallaci yayin da masallata ke gudanar da ibada acikin masallacin a kauyen Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kimanin mutane 17 ne suka rasa rayukansu a wannan lamari inda wasu kuma suka samu raunuka daban-daban kuma a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano.