Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayen waɗanda aka zaɓa domin shugabantar hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma (NWDC) ga majalisar dattijai domin tantancewa.
Wannan na biyo bayan sanya hannu kan ƙudirin dokar kafa NWDC da shugaban ya yi a ranar 24 ga Yuli, 2024, a matsayin muhimmin mataki wajen kafuwar hukumar.
- Hajji 2024: Kimanin Mutane 1,301 Ne Suka Rasu Saboda Tsananin Zafi Da Zuwa Hajji Ta Barauniyar Hanya – Saudiyya
- Zaben Gwamnan Edo: Nasarar Okpebolo Manuniya Ce Ga Yadda ‘Yan Nijeriya Ke Jin Dadin APC – Tinubu
Sunayen waɗanda aka naɗa sun haɗa da:
Shugaba: Ambasada Haruna Ginsau (Jigawa)
MD/CEO: Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano)
Mambobi:
Dr. Yahaya Umar Namahe (Sokoto)
Hon. Aminu Suleiman (Kebbi)
San. Tijani Yahaya Kaura (Zamfara)
Hon. Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil (Kano)
Shamsu Sule (Katsina)
Nasidi Ali (Jigawa)
Hukumar za ta mayar da hankali wajen samar da ci gaban tattalin arziki, bunƙasa rayuwa da cigaban zamantakewa a yankin Arewa Maso Yamma.