Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tura sabon jerin sunayen mambobin hukumar kula da ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) zuwa majalisar dattijai don amincewa.
A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an maye gurbin wasu daga cikin sunayen da aka fara turawa.
- Tinubu Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Rikicin Manoma Da Makiyaya A Nijeriya
- Tinubu Ya Amince Da Biyan Kuɗin Kafa Cibiyar Yaɗa Labarai Ta UNESCO
Shugaban da aka zaɓa yanzu shi ne Alhaji Lawal Samai’la Abdullahi, sai kuma Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji wanda zai ci gaba da riƙe muƙamin Darakta Janar da Shugaba.
Hakanan, Tinubu ya nada Hon. Emeka Atuma a matsayin shugaban Hukumar Ci Gaban Kudu maso Gabas (SEDC), kuma ya tura sunayen wasu mambobin na NWDC daga yankuna daban-daban na Nijeriya.