Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’ar nan ya sanar da nadin kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Shugaban kasa ya kuma nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Sanata. Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
- Tinubu Ya Shiga Wata Gana Wa Da Gwamnonin Jam’iyyar APC A Abuja
- Yanzu-yanzu: Tinubu Na Ganawa Ta Farko Da Shugabannin Tsaro
A ganawar da ya yi da gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki, shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka, George Akume, matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
Sanarwar nadin ta fito ta hannun daraktan yada labaran shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye a yau Juma’a 02, ga watan Yunin 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp