Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Ola Olukoyede a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) na tsawon shekaru hudu a matakin farko, har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Alhamis.
- Gwamnatin Bauchi Ta Kori Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Wikki Tourist
- Jirgin Sojoji Ya Yi Wa ‘Yan Ta’adda Luguden Wuta A Zamfara
Ngelale ya ce Olukoyede lauya ne wanda ke da gogewa sama da shekaru 22 kuma kwararre ne.
“Yana da gogewa sosai a harkokin hukumar EFCC, inda a baya ya rike mukamin shugaban ma’aikatan hukumar (2016-2018) da kuma sakataren hukumar (2018-2023). Don haka, ya cika sharudan da doka ta gindaya na nada shi a matsayin Shugaban Hukumar EFCC.
“Nadin Olukoyede ya biyo bayan dakatar da Mista Abdulrasheed Bawa,” in ji shi.
Bugu da kari, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce shugaba Tinubu ya amince da nadin Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tsawon shekaru biyar a matakin farko, har sai an majalisar dattawa ta tabbatar da shi.
“Muhammad Hassan Hammajoda ma’aikacin gwamnati ne wanda ya kware a harkar hada-hadar kudi na gwamnati wanda ya yi digirin digirgir a fannin lissafi a jami’ar Maiduguri da kuma digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci.
“Ya fara aiki a matsayin malami a Federal Polytechnic, Mubi. Daga nan ne ya shiga aikin banki, ciki har da wanda ya yi nasara a bankin Allied da Standard Trust Bank.
“Shugaba Bola Tinubu ya dorawa sabon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati (EFCC) aiki domin tabbatar da amincewar da aka basu a wannan muhimmin aiki na kasa a matsayin sabon yaki da cin hanci da rashawa da ake yi ta hanyar sake fasalin hukumomi a bangaren yaki da cin hanci da rashawa,” in ji shi.