Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban ciki har da Mallam Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na musamman.
Wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, daraktan yada labarai a fadar shugaban Najeriya ya fitar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da nade-naden da suka haÉ—ar da Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara kan harkar ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare.
- Yariman Bakura Ya Taya Akpabio Murnar Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Jos 7
Akwai kuma Mallam Ya’u Darazo a mukamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da hulda tsakanin gwamnatoci.
Haka zalika, Tinubu ya amince da nada Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara na musamman kan manufofin kudi.
Akwai kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin makamashi, inda Tinubu ya naÉ—a Misis Olu Verheijen.
Ƙarin masu bayar da shawarar har da Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudin shiga.
An kuma naÉ—a Dokta Salma Ibrahim Anas a mukamin mai ba da shawara ta musamman a fannin kula da lafiya.
Sai kuma Mista John Ugochukwu wanda aka nada mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari.