Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta rage kudaden haraji da ake karba daga hukumomin da ke karkashin ma’aikatar sufurin jiragen sama, daga kashi 50 da ake karbar zuwa kashi 20.
Bayanin ya nuna cewa, kungiyoyin kwadago a ma’aikatar sun yi barazanar shiga yajin aiki a fadin tarayyar Nijeriya in gwamnati bata dakatar da daukar matakin cire musu kashi 50 na kudin da suke tattarawa na shigar su a matakin ma’aikata ba zuwa kashi 20, musamman ganin rashin yin haka yana kawo cikas ga tafiyar da ayyukansu.
- Kudirin Wa’adin Shekaru 6 Ga Shugaban Kasa Ya Tsallake Karatu Na Farko
- Durkushewar Kamfanoni Ta Kara Rashin Aikin Yi Tsakanin Matasa
In har an bari kungiyar kwadagon ta shiga zanga-zanga da yajin aiki zai iya shafar tashi da saukar jiragen sama a kasar nan.
Sanawar da ta fito daga daya daga cikin maitaimakan Ministan Sufurin Jiragen Sama, Saka Gbenga, ya ce, wannan ragewar da aka yi ya nuna Shugaba Bola Tinubu yana da kudurin ganin an farfado da bangaren sufurin jiragen saman Nijeriya.
Saka ya kuma kara da cewa, Shugaban kasa zai tattauana tare da samar da fahintar juna tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago, za kuma a samu warware matsalar na rashin fahimta daidai da dokokin da ya tanadi hukumomin na bangaren ma’aikatar sufurin jiragen sama.
“Wannan shirin ya yi daidai da mastayar Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo inda yaba wa ma’aikatan da masu ruwa da staki tabbacin gwamnati za ta hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki wajen samar da karbabbiyar mafita da kowa zai yi murna da shi.”
Tun da farko ministan ya bayyana a asusunsa na D cewa, gwamnati ta lura tare da amincewa da korafin na yadda ake cire musu kudade daga asusun tara harajin su na IGR, an kuma yanke shawarar dubawa don a samu fafado da kayan aiki da jin dadin ma’aikata.
Ya kuma kara da cewa, “Muna kira ga dukkan kungiyoyin ma’aikata su natsu tare da kwantar da hankalinsu musamman ganin gwamnati na kokarin ganin ta warware dukkan matsalolin da suka bijiri da su.”