Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa Sin da Afirka, wato FOCAC na shekarar 2024 tare da gabatar da jawabi a ran 5 ga watan Satumba mai zuwa. Yayin taron, Xi Jinping zai shirya liyafa don tarban shugabannin kasashen Afirka da wakilan kungiyoyin yankin Afirka da na duniya wadanda za su halarci taron da sauran ayyuka. (Amina Xu)
Talla