A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin Alkalin alkalai ta Nijeriya (CJN).
An gudanar da bikin ne a fadar shugaban kasa, Aso Rock da ke Abuja.
- ‘Yan Kasuwa Daga Amurka Na Shirin Zuba Hannu Jari A Jihar Nasarawa – Gwamna Sule
- Sin Ta Kaddamar Da Gagarumin Bikin Ba Da Lambobin Yabo Na Kasar Sin
Nadin Kekere-Ekun ya biyo bayan amincewar da majalisar dattawan Nijeriya ta yi a makon da ya gabata.
Kudirat ta zama Alkalin Alkalan Nijeriya ta 23 kuma mace ta biyu da ta rike wannan mukami.
Mai shari’a Kekere-Ekun ta kasance mai rikon mukamin CJN tun watan Agusta lokacin da aka sanar da nadin nata biyo bayan ritaya din da magabacin ta, Mai shari’a Olukayode Ariwoola ya yi.