Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya amince da rushe ma’aikatun Neja Delta da Ma’aikatar wasanni a wani yunƙuri na sauya fasalin ma’aikatun tarayyar Nijeriya.
Ya bayyana matakin ne yayin taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), a Abuja.
- Gidauniya Da Gwamnatin Zamfara Sun Tallafa Wa Mata 200 Da Kajin Kiwo
- An Watsa Shirin Bidiyo Zagaye Na 3 Mai Taken “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So” A Rasha
Ya sanar da sabuwar Ma’aikatar Raya Yanki a matsayin wace za ta maye gurbinsu da kula da dukkan kwamitocin raya yankin.
Wannan ya hada da hukumomi irin su Hukumar Raya Neja-Delta da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma da Hukumar Raya Yankin Kudu Maso Yamma da Hukumar Raya Arewa maso Gabas da nufin daidaita ayyukan ci gaban yankunan a faɗin kasar nan.
A halin yanzu hukumar wasanni ta ƙasa za ta karbi ayyukan ma’aikatar wasanni inda za ta ɗauki nauyin gudanarwa da bunkasa harkokin wasanni a Nijeriya.
Bugu da kari, Majalisar Zartaswan ta amince da hade ma’aikatar yawon bude ido da ma’aikatar al’adu da tattalin arziki duk a ƙoƙarin ƙarfafawa tare da ɓunƙasa harkokin yawon bude ido da al’adu.