Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi.
Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar.
- Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC
- Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje
A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da cigaban zamani da ake yi wa hukumar Kwastan, da aiwatar da tsarin “National Single Window Project” da kuma cika alƙawuran Nijeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar cinikayyar Afrika (AfCFTA).
“Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp