Shugaba Tinubu ya amince da nadin Hon. Zacch Adedeji, a matsayin sabon shugaban riko na hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS).
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa, shugaban kasa ya umurci tsohon shugaban na FIRS, Muhammad Nami, da ya hanzarta ci gaba da hutunsa na watanni uku kafin ya yi ritaya, kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati (PSR) 120243 ta tanada. Hakan zai kai cika wa’adin ritayarsa daga aiki a ranar 8 ga Disamba, 2023.
- Gwamnoni Za Su Gana Da CBN, EFCC, ICPC, FIRS Kan Tattalin Arziki
- Remi Tinubu Ta Bada Tallafin Naira Miliyan N500 Ga Iyalai 500 Da Rikici Ya Shafa A Jihar Filato
Adedeji ya ce, an nada sabon shugaban a matsayin mukaddashin hukumar na tsawon kwanaki 90 kafin a tabbatar da shi a matsayin babban shugaban hukumar tara haraji ta tarayya na tsawon shekaru hudu (4) a matakin farko.
“Hon. Zacch Adedeji ya yi digiri na farko a fannin lissafin kudade daga Jami’ar Obafemi Awolowo.
“Ba jimawa ya rike mukamin a matsayin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga, ya kuma ataba zama kwamishinan kudi na jihar Oyo da kuma rike matsayin babban sakataren zartarwa / shugaban hukumar bunkasa sukari ta kasa (NSDC).
“Tuni Shugaban Kasa, ya bayar da umarnin wannan sabon nadin, inda zai fara aiki nan take,” Cewar Ngelale.