Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci ma’aikatar shari’ar ta yi aiki da majalisar dokoki domin gyara ababen da ke janyo ce-ce-ku-ce a kudirin gyaran dokar haraji.
Ministan Yada Labaru, Mohammed Idris cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Tinubu yana maraba da duk wani gyara da za a yi wa dokar.
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar Sin
- Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudurinsa Na Bai Wa Ɓangaren Shari’a ‘Yanci Don Samar Da Adalci A Zamfara
“Shugaba Tinubu na maraba da duk wani gyara da zai sauya duk wata sadara da ke jawo cece-kuce a kudirin.”
Shugaba Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin da kudurorin ne makonnin da suka gabata.
Sai dai gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya yi zargin cewa jihohin Legas da Ribas ne kawai za su amfana idan aka sauya dokar harajin
Gwamnan ya bayyana haka ke a gidan talabijin na Channels, inda ya ce matukar dokar ta tabbata Jihohin Arewa ba za su iya biyan albashi ba.
A gefe guda, ita majalisar dokokin Jihar Kano, ta ki aminta da dokar, inda ‘yan majalisunta suka yi zargin akwai lauje cikin nadi game da dokar.
Dokar gyaran haraji ta bar baya da kura, inda ake ci gaba da tafka muhawara musamman a Arewacin Nijeriya.