Biyo bayan cece-kuce da suka da jama’a ke ta famar yi, gwamnatin Tinubu ta umurci sake nazarin shirin bayar da tallafin kudi na Naira 8,000 da nufin samar da agaji ga magidanta masu karamin karfi don rage radadin cire tallafin man fetur.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya ce, gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar fifita bukatar ‘yan Nijeriya da jin dadinsu da tsaronsu fiye da bukatarta a karkashin shirin “Sabunta kwarin guiwa”, hakan ya sanya daukar matakin gaggawa.
Idan dai za a iya tunawa, bayan yanke shawarar dakatar da tallafin man fetur, gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin aiwatar da wani shiri na bayar da agaji, wanda za a dinga bayar da tallafin Naira 8,000 duk wata na tsawon watanni shida ga magidanta masu karamin karfi miliyan 12.
Sai dai shirin ya gamu da cece-kuce da suka, inda da dama ke nuna rashin jin dadi da kuma shakku kan tasiri da ingancin shirin.
Shugaba Tinubu ya bada muhimmanci kan ra’ayoyin jama’a, inda take ya yi biyayya ga ra’ayoyin jama’a kuma ya bada umarnin sake nazarin shirin bayar da tallafin cikin gaggawa.