Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin wai ana nuna bambanci wajen rabon ayyuka da naɗin muƙamai a ƙarƙashin shugabancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa babu wani yanki da aka ware, kowane ɓangare yana samun kulawa iri ɗaya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya faɗa a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, cewa gwamnatin Tinubu tana tafiya ne bisa gaskiya, adalci da daidaito wajen rarraba ayyuka da damarmaki.
- Kasar Sin Ta Inganta Wuraren Tunawa Da Tarihi Don Bikin Samun Nasara Kan Zaluncin Japanawa
- Ina Da Yaƙinin Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen 2027 — Wike
Ya ce manyan ayyukan raya ƙasa suna gudana a dukkan yankuna shida, ciki har da tituna, gadaje, layin dogo, wutar lantarki da kuma cibiyoyin kula da lafiya fiye da 1,000 da aka gyara a faɗin ƙasar.
A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604.
Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna amfana da manyan hanyoyi, layukan dogo da kuma hukumomin raya yankuna.
Ministan ya ce daga cikin muhimman ayyukan da ake aiwatarwa akwai Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gyaran layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da kuma Hanyar Gadar Neja ta 2.
Haka kuma, gwamnati ta samar da fiye da naira biliyan 250 don ayyukan jirgin ƙasa a Kano da Kaduna, yayin da ake gudanar da ayyukan layin dogo na Cikin gari a Legas da Ogun. Gaba ɗaya, an ƙiyasta cewa waɗannan ayyuka za su samar da fiye da ayyukan yi 250,000 a faɗin ƙasar.
Idris ya ƙara da cewa an farfaɗo da Tashar Wutar Lantarki ta Kaduna mai ƙarfin megawat 255, ana ci gaba da aikin iskar gas na AKK, tare da bunƙasa haƙo mai a yankin Kolmani (a Bauchi da Gombe).
Ya ce naɗin muƙaman da Shugaban Ƙasa Tinubu ya yi ya nuna haɗin kai, yana mai jaddada cewa abin da ke jagorantar shi shi ne ƙwarewa da kuma haɗin kan ƙasa.
Idris ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa Shirin Sabunta Fata zai ci gaba da tabbatar da daidaito a cigaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp