ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya

by Sadiq
11 months ago
Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada ƙudirinsa na inganta wutar lantarki a Nujeriya yayin da yake jawabi a wani taron shugabannin ƙasashen Afirka a Arusha, Tanzaniya.

Taron ya mayar da hankali kan yadda za a samar wa mutane miliyan 300 wutar lantarki nan da shekarar 2030.

  • Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu Da Aiki Tuƙuru
  • CMG Ya Yi Nunin Fitilu A Jikin Manyan Gine-Ginen Afirka Ta Kudu Da UAE

Tinubu ya ce, da taimakon Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), wanda ya bayar da tallafin dala biliyan 1.1, Nijeriya za ta ƙara samar da wutar lantarki ga mutane miliyan biyar nan da shekarar 2026.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, za a kashe dala miliyan 200 domin samar da wuta ga mutane dubu 500 kafin ƙarshen shekarar 2025.

Shugaban ya kuma bayyana cewa suna shirin amfani da tallafin dala miliyan 750 daga Bankin Duniya don inganta ƙananan tashoshin samar da wuta, wanda zai amfanar da mutane miliyan 16.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Tinubu ya gode wa shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, saboda ƙoƙarinsu na samar da karin wutar lantarki a Afirka.

Ya kuma ce yadda masu zuba jari ke gamsuwa da shirye-shiryen gwamnatinsa ya sa aka samu jarin dala biliyan shida a ɓangaren samar da makamashi a shekarar da ta gabata.

Hukumar IFC ta sanar da cewa za ta saka dala miliyan 70 domin taimaka wa ‘yan kasuwa su samar da wutar lantarki ta hanyoyin da ba sa gurɓata muhalli.

Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na buƙatar aƙalla dala biliyan 23.2 domin inganta ɓangaren wutar lantarki da tabbatar da wadatarta ga al’umma.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da dama, ciki har da shugabannin Afirka ta Kudu, Ghana, Rwanda, Tanzania, da kuma mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed.

Sauran mahalarta sun haɗa da shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Ademola Lookman Ba Zai Buga Wasan Atalanta Da Barcelona Ba

Ademola Lookman Ba Zai Buga Wasan Atalanta Da Barcelona Ba

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.