Tikitin Kirista Da Musulmi Ba Zai Kai Mu Ga Nasara Ba, Tinubu Ya Yi Daidai Na Zabin Musulmi, Inji Tsohon Shugaban APC, Oshiomhole
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya sanya kafa ya shure sukar da wasu ke ta yi ga zabin Musulmi da dan takarar shugaban Shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin abokin takararsa.
Oshiomhole ya ce, lokaci ya yi da za a cire wani kabilanci ko addinanci a maida hankali wajen zabin wadanda suka dace domin ceto Nijeriya daga halin da take ciki.
Adams wanda ke ganawa da TVC ya nuna gamsuwarsa da tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta yi, ya kara da jinjina wa Tinubu bisa daukan wannan kyakkyawar matakin na zabin tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.
Ya ce, “Wasu jam’iyyun adawa ma suna tsoma bakinsu kan muhawarar tikitin musulmai biyu, amma ni kam na gamsu da matakin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dauka.”
Oshiomhole ya gamsu da zabin Shettima ne bisa dacewa da cancantar sa gami da irin nasarorin da ya cimma a baya, “Bai kamata ya zama kamar al’ada ba. Na gamsu da nagartar Shettima. Kuma nasarorin da ya cimma a rayuwarsa tabbas zai tabuka abun a zo a gani a matsayin matakin Shugaban kasa.”
Ya kara da cewa, kyawawan tarihin da Shettima ke da shi, zai yi kara wa APC tagomashi a zaben 2023, kuma ba ma maganar kirista ko Musulmi ya dace a maida hankali a APC ba, inda ya ce, “Wadanda za su iya kawo wa jam’iyyar nasara ya kamata a fi la’akari da su. Don haka wannan matakin shine daidai muddin nasara ake nema.”
Dangane da masu cewa ana neman karfafan addini ne a lamarin, Tsohon Shugaban APCn ya ce Tinubu ko a gidansa ma bai addinantar da kowa ba, “Don haka ba wani abu na damuwa a wannan lamarin. Sun ce ana kokarin maida lamarin na addini, to Tinubu ko iyalansa bai iya addinantar da su ba. Ko kun ga ya addinantar da iyalansa? Matarsa kirista ce kuma Fasto.”