Shugaba Bola Tinubu ya daga likkafar Babban Hafsan Sojin Kasa Nijeriya na riko, Olufemi Oluyede zuwa Laftanar Janar.
Kakakin fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar da karin girman a fadar shugaban kasa.
- Real Madrid: Me Ke Faruwa Ne A Santiago?
- Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Wasu Kan Yunƙurin Dakatar Da Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomin Kano
Matukar Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi zai kasance cikakken babban hafsan sojin da zai maye gurbin Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a mataki na dindindin.
An daga likkafarsa ne kwanaki bayan da Shugaba Tinubu ya nada shi mukamin a mataki na riko.
A nasa bangaren, Laftanar Janar Oluyede ya bayyana matukar godiya tare da martaba lamarin.
Ya jaddada aniyar dabbaka muradan Laftanar Janar Taoreed Lagbaja tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin Nijeriya.