Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai kai ziyara Jihar Nasarawa a wannan wata domin ƙaddamar da sabon kamfanin sarrafa battirin lithium.
Gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya bayyana hakan bayan ganawarsa da shugaban ƙasa a fadar gwamnati da ke Abuja. Ya ce kamfanin, wanda ƴan kasuwa daga ƙasar Sin suka gina a ƙaramar hukumar Nasarawa, ya fi girma sau biyu kan wanda aka buɗe a shekarar 2023, wanda ke da ikon sarrafa ton 3,000 na albarkatun lithium.
- Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin
- Kungiyar Kare Shirye-shiryen Tinubu Ta Nemi A Dakatar Da Shugaban Kamfanin NNPCL
A cewar Gwamna Sule, shugaban ƙasa zai kaddamar da wannan masana’anta ne bayan dawowarsa daga hutun makonni biyu da yake yi a ƙasar Faransa.
Ya bayyana cewa aikin na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na dakatar da fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su a cikin gida ba, tare da bunƙasa masana’antu a cikin ƙasa.
Gwamna Sule ya kuma ce sauya sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin Tinubu ta yi, musamman cire tallafin man fetur da haɗa tsarin musayar kuɗin ƙasa, sun ƙarawa jihohi kuɗi tare da jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp