Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bibiyi kwazon ministocinsa a ranar 29 ga Mayu, yayin da gwamnatinsa ta cika shekaru biyu a ofis, kamar yadda majiyoyi daga fadar shugaban kasa suka tabbatar da hakan.
Bibiyan kwazon ministocin, wanda ofishin bayar da sakamako da hadin gwiwa ta tsakiya (CDCU) da ke karkashin fadar shugaban kasa zai gabatar da cikakken bayanai kan nasarorin kowace ma’aikata a cikin rubu’in farko na shekara ta 2025.
- Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai
- Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin
Majiyoyi sun bayyana cewa ministocin sun gabatar da shaidun ayyukansu da shirinsu ta hanyar intanet a makon jiya, inda a yanzu aka kammala tantancewa ta hannun CDCU. Ana sa ran za a mika rahoton karshe ga Shugaba Tinubu kafin ranar bikin cika shekara biyu a kan karagar mulkin Nijeriya
“Jami’an na ma’aikatu daban-daban sun dora rahotannin ayyukansu da shirye-shiryensu a shafin da CDCU ta bayar,” in ji wani dan wani daga fadar shugaban kasa. “Wannan yana bisa ga abubuwan da aka tsara wa ma’aikatun.”
Auna kwazon ya biyo bayan umarnin da Tinubu ya bayar a lokacin taron majalisar bibiyan ma’aikatu na watan Nuwamba 2023, inda ya bayyana cewa za a guda kwazon ministoci bisa ga ayyukansu.
“Idan ka yi kwao sosai, babu abin da za ka ji tsoro. Idan ba ka yi kwazo ba, za mu biyiya. Idan ba ka yi komai ba, za ka bar mana aikinmu,” in ji shugaban kasa.
Masu ruwa da tsaki sun ce wasu ministoci, musamman a cikin muhimman sassa, suna cikin bincike yayin da Tinubu ke shirin yanke hukunci a kan inganta majalisar ministocinsa.
A yanzu dai ana zuba ido a gani ko dai Tinubu zai gudanar da sauye-sauye a majalisar ministocinsa cikin gaggawa ko kuma zai jinkinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp