Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa za ta nemi bashin kudi har naira tiriliyan 13 domin cike gibin da ke cikin kasafin kudin shekarar 2025.
Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ne, ya bayyana hakan bayan taron majalisar tattalin arziki da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Maguire Na Son Sabunta Kwantiraginsa A Manchester United
- CBN Zai Hukunta Bankuna Masu Haddasa Karancin KuÉ—i
Ya ce bashin shi ne mafita ga matsalar gibin kasafin kudin bana.
A cewarsa, jimillar kasafin kudin na 2025 zai kai naira tiriliyan 47 da biliyan tara, wanda hakan ya habaka da kashi 36.8 idan aka kwatanta da kasafin 2024.
A cikinsa, kudaden gudanar da ayyuka sun kai naira tiriliyan 34 da biliyan takwas.
Gibin da aka gano a kasafin kudin ya tsaya kan naira tiriliyan 13, wanda ya yi daidai da kashi 3.39 na tattalin arzikin Nijeriya (GDP).
Edun, ya ce kasafin kudin ya dogara ne kan irin ci gaban da Nijeriya ta samu a cikin watanni 18 na shugabancin Bola Tinubu.