Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu zuwa birnin N’Djamena na Jamhuriyar Chadi domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Idriss Mahamat Deby Itno.
Bikin rantsar da shi ya biyo bayan ayyana shugaba Deby a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon watan Mayu da kotun tsarin mulkin kasar ta Chadi ta tabbatar.
- Lookman Ya Zura Kwallo Uku Rigis Yayin Da Atalanta Ta Lashe Kofin Europa LeagueÂ
- Ba Za A Yi Gagarumin Bikin Cikar Gwamnatin Tinubu Shekara ÆŠaya Ba, In ji Ministan YaÉ—a Labarai
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, wasu manyan jami’an gwamnati ne za su raka shugaba Tinubu kuma zai dawo bayan kammala bikin.
Deby, shugaban mulkin sojan Chadi, ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu ne, da kashi 61 na kuri’un da aka kada, a cewar sakamakon karshe da aka sanar.
Sai dai babban abokin hamayyarsa Succes ya kalubalantar sakamakon zaben.
A baya ma shugaba Tinubu ya halarci bikin rantsar da shugaba Bassirou Faye na kasar Senegal wanda ya lashe zaben shugaban kasar a baya-bayan nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp