Shugaban Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa Birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea, inda zai kai ziyarar aiki ta kwanaki uku.
Zai kai ziyarar ne domin girmama gayyatar da shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya yi masa.
- An Samu Ƙaruwar Garkuwa Da Mutane A Nijeriya – Rahoto
- Gwamnati Ta Janye Dokar Hana Fita A Kaduna Da Zariya
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce shugaban zai gana da shugaban kasar Equatorial Guinea a fadar shugaban kasar.
Shugabannin biyu za su gana tare da kulla yarjejeniya kan abin da ya shafi man fetur da iskar gas da kuma tsaro.
Shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar da sauran ministocinsa wadanda za su sanya hannu wajen rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da za a yi tsakanin kasashen biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp