Mataimakiya ta musamman ga Shugaban Kasa Bola Tinubu a kan tsare-tsaren gwamnati, kuma ma isa ido a kan yadda masu rike mukaman gwamnati ke tafiyar da ayyukansu, Hadiza Bala Usman, ta bayyana cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba za iy watawata ba wajen sauke duk ministan da ya gaza gudanar da ayyukansa yadda kamata.
Hadiza Bala Usman ta ce, Shugaba Tinubu a tsaye yake wajen ganin ya cika alkawarinsa na inganta rayuwar al’ummar Nijeriya kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe.
- Xi Jinping Ya Yi Jawabi Ta Kafar Bidiyo Ga Liyafar Murnar Cika Shekaru 60 Da Kulla Huldar Diplomasiyya A Tsakanin Sin Da Faransa
- Gwamnatin Zamfara Za Ta Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata
Ta yi wannan bayanin ne a taron da aka shirya wa jami’ai da aka tura ma’aikatun gwamnati don sa ido a kan yadda ministocin ke gudanar da aikin su, wanda aka yi a garin Uyo, babbar birnin Jihar Akwa Ibom .
Ta nemi jami’an su rike aikin su da gaskiya don a tabbatar da samun nasarar da shugaban kasa ya kudurta.
“Ya kamata kowa ya fahimci cewa shugaban kasa da gaske yake yi na cika alkwarin da ya dauka na yi wa al’ummar Nijeriya aiki, a kan haka za mu rinka duba ayyukan ministoci, duk ministan da ya gaza kai bantensa za a sauke shi,” in ji ta.