A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja domin fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Faransa domin amsa goron gayyatar da shugaba Emmanuel Macron ya yi masa.
Ziyarar wadda za ta mayar da hankali kan karfafa dangantakar siyasa, tattalin arziki, da al’adu da samar da karin damammaki na hadin gwiwa, musamman a fannin noma, tsaro, ilimi, kiwon lafiya, harkar makamashi, ci gaban matasa da ayyukan yi, kirkire-kirkire, ana kyautata zaton cewa, za ta samar da gagarumar nasara ga Nijeriya.
- Tinkarar Sauyin Yanayi Na Bukatar Gaggauta Sauke Nauyin Da Ya Rataya A Wuyan Kasa Da Kasa
- Gwamnatin Kebbi Ta Dakile Yunkurin Lakurawa Na Satar Shanu
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu da mai dakinsa, Sanata Oluremi Tinubu, za su isa kasar a ranar Alhamis a gidan tarihi na sojojin Faransa, ‘Les Invalides da Palais de l’Élysée,’ mai shekaru 350 wanda Macron da matarsa, Brigitte za su tarbe su, wanda daga bisani za su shiga cikin tattaunawar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, manyan jami’an gwamnati za su raka shugaba Tinubu a wannan tafiya.