• English
  • Business News
Friday, August 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Zai Yi Amfani Da Dokar Ta-ɓaci Wajen Tsoratar Da Gwamnoni Gabanin Zaben 2027 – Amaechi

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
in Siyasa
0
Tinubu Zai Yi Amfani Da Dokar Ta-ɓaci Wajen Tsoratar Da Gwamnoni Gabanin Zaben 2027 – Amaechi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya soki ayyana dokar ta-baci da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas, inda ya bayyana hakan a matsayin wata manufa ta siyasa da nufin tsoratar da gwamnonin da ba za su goyi bayan tazarcensa ba a 2027.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 18 ga watan Maris ne Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewa an dade ana fama da rikicin siyasa da barnatar da albarkatun man fetur a matsayin muhimman dalilai. Matakin ya kai ga dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida. A madadinsu, Tinubu ya nada Ibok-Ete Ibas a matsayin mai kula da jihar.

  • Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027
  • Gwamnatin Edo Za Ta Binciki Kisan Matafiya ‘Yan Arewa A Jihar

Sai dai matakin ya haifar da adawa mai tsanani, inda kungiyoyin farar hula da kuma kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) suka yi Allah wadai da lamarin, wanda suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan.

Har ila yau, Amaechi, a wata hira da DW Africa, ya zargi Shugaba Tinubu da yin amfani da dokar ta-baci a matsayin makamin rufe bakin gwamnonin ‘yan adawa da kuma kara karfafa mulki.

“Lamarin dokar ta-baci ya kasance ne tsakanin shugaban kasa da ministan babban birnin tarayya. Shugaban kasa na son a ci gaba da darewa a kan mulki. Suna so su tsoratar da gwamnonin da ba za su goyi bayansu ba a 2027. Don haka, ana yada jita-jita a ko’ina cewa idan ba ku yi hankali ba, shugaban kasa zai tsige ku,” in ji Amaechi.

Labarai Masu Nasaba

PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi

Jagora A ADC Ya Ƙaryata Zargin Atiku Ya Kankane Komai A Jam’iyyar

Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka.

“Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya batun sassan kasar da ake fama da rashin tsaro? Shugaban kasar yana cewa su ma su kafa masa dokar ta-baci a kansa. Ba za su iya ba, saboda shi shugaban kasa ne da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, babu wanda zai iya sanya masa dokar ta-baci, saboda akwai rashin tsaro mai tsanani a arewa maso gabas, arewa maso yamma, hatta a kudu maso gabas da kudu maso yamma, amma ba a saka dokar ta-baci ba sai a Jihar Ribas.”

Amaechi ya jaddada cewa alhakin tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya, ba gwamnonin jihohi ba, wanda hakan ya sa dakatarwar Fubara ba ta dace ba.

“Gwamnan Ribas ba shi da alhakin tsaro, ya rataya a wuyan shugaban kasa, to me zai sa a hukunta mutumin da bai aikata wani laifi ba?” Ya tambaya.

Tsohon gwamnan na Ribas ya zargi Tinubu da saba ka’idojin tsarin mulki na yadda za a cire gwamna daga mukaminsa.

“Shugaban ya yanke hukunci ne ta wajen kundin tsarin mulki. Sashe na 188 ya bayyana yadda gwamna zai bar mulki, ko dai ya mutu, ko murabus, ko kuma a tsige shi. Amma bai ce wata rana ka farka ba, wani mutum da ake kira shugaban Nijeriya zai fid da ka daga mulki, wanda hakan ya saba wa dimokuradiyyar Nijeriya.”

Amaechi ya yi kira ga mazauna Ribas da su bijire wa dokar ta-baci, sannan ya bukace su da su yi zanga-zangar lumana wanda dimokuradiyya ta amince da shi.

Da yake magana kan rikicin siyasar da ke faruwa tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Fubara, Amaechi ya yi zargin cewa rikicin kudi ne kawai.

“Abun da ke faruwa a tsakanin Gwamnan Jihar Ribas na yanzu da Ministan Babban Birnin Tarayya, shi ne batun raba kudi, idan ba haka ba, mene ne na rigima? ‘Yan Nijeriya ba sa son cin hanci da rashawa a wannan lokaci, ban ga wani a kan titi yana tambayar ko mene ne matsalar ba, ko su biyun za su iya magana da jama’a su fada mana matsalar?”

Amaechi ya koka da yadda a yanzu Jihar Ribas na karkashin mulkin soja ne, inda ta hana ‘yan kasar cin ribar dimokuradiyya.

“Yanzu an hana mu cin gajiyar dimokuradiyya. Jihar Ribas ce kadai jihar da ba ta jin dadin dimokuradiyya a halin yanzu, sun kakaba mana mulkin soja da karfin tsiya,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: DokaZabe
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kasar Sin Na Nuna Damuwa Sosai Kan Harin Intanet Da Aka Kai Mata

Next Post

Tinubu Da Kwankwaso Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Dokta Idris Dutsen Tanshi

Related

PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi
Manyan Labarai

PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi

3 days ago
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku
Manyan Labarai

Jagora A ADC Ya Ƙaryata Zargin Atiku Ya Kankane Komai A Jam’iyyar

3 days ago
INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027
Siyasa

INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027

4 days ago
Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
Siyasa

Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027

5 days ago
Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10
Siyasa

Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10

5 days ago
ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya
Siyasa

ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya

6 days ago
Next Post
Tinubu Da Kwankwaso Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Dokta Idris Dutsen Tanshi

Tinubu Da Kwankwaso Sun Yi Ta'aziyyar Rasuwar Dokta Idris Dutsen Tanshi

LABARAI MASU NASABA

Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare

Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare

August 14, 2025
NLC Ta Baiwa Gwamnati Kwanaki 7 Don Magance Badaƙalar Satar Kuɗin Ma’aikata

NLC Ta Baiwa Gwamnati Kwanaki 7 Don Magance Badaƙalar Satar Kuɗin Ma’aikata

August 14, 2025
Sashen Aikewa Da Kunshin Sakwanni Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni 7 Na Farkon Bana

Sashen Aikewa Da Kunshin Sakwanni Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni 7 Na Farkon Bana

August 14, 2025
Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe

Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe

August 14, 2025
Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka

Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka

August 14, 2025
Gwamnati Na Ƙoƙarin Tsoratar Da Ni Don In Shiga APC – Sanata Tambuwal

Gwamnati Na Ƙoƙarin Tsoratar Da Ni Don In Shiga APC – Sanata Tambuwal

August 14, 2025
Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin

Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin

August 14, 2025
Gidauniya Ta Rabar Da Buhun Takin Zamani 6,000 Ga Manoma A Bauchi 

Gidauniya Ta Rabar Da Buhun Takin Zamani 6,000 Ga Manoma A Bauchi 

August 14, 2025
Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 139, Sun Cafke 132 A Cikin Sati 2 —Hedikwatar Tsaro

Sojoji Sun Kama Mutane 107 Da Ake Zargi, Sun Ceto Mutane 20 A Cikin Mako Guda – DHQ

August 14, 2025
‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin

‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin

August 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.