Domin kawo karshen zanga-zangar da ake yi a fadin kasar na sakamakon yanayin tattalin arziki da ake fama da shi, shugaba Bola Tinubu zai yi wa al’ummar kasar nan jawabi a kafafen watsa labarai a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024, da misalin 7 na safe.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Cif Ajuri Ngelale, ya sanya wa hannu a yammacin ranar Asabar.
- Kudurin Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Ya Shafi Manyan Tsare-Tsare Tare Da Matakai Na Zahiri
- Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Ya ce an umarci gudajen talabijin, rediyo, da sauran kafafen yada labarai da su watsa shirin ka-tsaye.
“Za a sake maimaita shirin a NTA da FRCN da misalin karfe 3 na yamma da 7:00 na daren wannan rana,” in ji Ngelale.
Wannan dai ba zai rasa nasaba da zanga-zangar da ake gudanar a fadin Nijeriya ba.
A wasu yankunan kasar dai al’amura sun tabarbare, inda lamarin ya zama tashe-tashen hankula.