Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Jihar Legas zuwa Jos, babban birnin Jihar Filato, a ranar Asabar, 4 ga watan Oktoba, domin halartar jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Shugaban Ƙasa zai kuma gana da shugabannin coci daga Arewacin Najeriya a hedikwatar COCIN da ke Jos.
Ya ƙara da cewa Tinubu zai koma Legas a ranar bayan kammala ziyarar.












