Tsohon dan wasan kasar Jamus, Toni Kroos, ya kafa tarihin lashe gasar cin kofin duniya na kungiyoyi bayan da a ranar Asabar Real Madrid ta lashe gasar FIFA Club World, bayan doke Al Hilal 5-3 a Morocco.
Toni Kroos yana cikin ‘yan wasan da suka buga mata karawar, wanda ya dauki kofi na shida na zakarun nahiyoyin duniya ya fara daukar daya a lokacin da yake Bayern Munich, yanzu ya ci na biyar tare da Real Madrid, wadda ta lashe na takwas jimilla.
- DSS Ta Bankado Shirin Boko Haram Na Kai Wa Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Hari
- Maganin Ciwon Sanyi A Saukake
Wasu ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Real Madrid da suka dauki Club World Cup biyar a kungiyar sun hada da Karim Benzema da Nacho da Dani Carbajal da kuma Luca Modric.
Kofi na biyu kenan da Real Madrid ta lashe a kakar nan, bayan Uefa Super Cup kuma Real Madrid wadda take ta biyu a bana a teburin La Liga da tazarar maki 11 ta yi rashin nasara a Spanish Super Cup a watan Janairu a hannun Barcelona a Saudia Arabia.
Real Madrid ta kai wasan karshe a Club World Cup, bayan cin Al Ahly 4-1 ranar Laraba, ita kuwa Al Hilal nasara ta yi a kan Flamengo 3-2 ranar Talata sannan Real Madrid ita ce ke rike da Champions League a Turai, ita kuwa Al Hilal ta Saudi Arabia ita ta lashe na zakarun Asia.