Tottenham Hotspur tana tuntubar Barcelona wajen ganin ta dauki Ansu Fati amma akwai yiwuwar Chelsea na iya kutsawa cinikin.
Dukkansu Spurs da Blues suna neman karfafa ‘yan wasansu kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a ranar Juma’a.
- Ministan Wajen Sin Ya Tayawa Takwaransa Na Najeriya Murnar Kama Aiki Ta Wayar Tarho
- Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Gabon
Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino, yana matukar bukatar siyan dan wasan gaba wanda zai iya taka leda a matsayin dan wasan gefe ko lamba 10.
Barcelona na bukatar bin ka’idojin Financial Fair Play kuma suna tunanin siyarwa ko ba da rancen Fati a wannan bazarar don taimaka musu yin hakan.
Ficewar Fati daga Barcelona zai bai wa kungiyar ta La Liga damar dauko Joao Felix daga Atletico Madrid.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp