Tsohon shugaban Amurka kuma dan takarar jamiyyar Republican a zaben kasar mai zuwa Donald Trump da mataimakiyar shugaban kasar kuma ‘yar takarar jamiyyar Democrat, Kamala Harris sun gwabza a kan batun tattalin arziki da ‘yancin zubar da ciki da kuma manufar shige da fice a muhawararsu ta farko a kan zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.
Muhawarar wadda sau da dama ta kan karkata ga suka da cin dunduniyar juna, ta tabo bangarori da dama da suka kama daga abubuwan da suka jibinci batun manufofi da waje da tattalin arziki.
- Sakon Da Aka Isar Game Da Yanayin Tekun Kudancin Kasar Sin Daga Wasu Taruka Uku
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
Muhawarar wadda ta kasance ta farko a tsakaninsu kasancewar ba su taba haduwa gaba da gaba ba ta fara ne da ban mamaki, inda Kamala Harris ta tunkari Donald Trump ta yi musabaha da shi a abin da za a ce musabaha ta farko a wata muhawar ta masu neman shugaban kasa tun 2016.
Muhawara dai ta kasance mai muhimmanci musamman ga ita Kamala Harris, wadda kuriar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa sama da kashi daya bisa hudu na masu zabe ke ganin ba su da masaniya sosai a kanta.
‘Yan takarar biyu sun bude muhawara ne da ta hanyar mayar da hankali kan batun tattalin arziki, bangaren da kur’iar jin ra’ayin jama’a ta nuna Trump ya fi dama.
Harris ta soki aniyar Trump ta sanya haraji mai yawa a kan kayayyakin waje, wanda shiri ne da ta kwatanta da haraji a kan masu matsakaicin samu, inda ta tallata shirinta na rage haraji ga iyalai da masu kananan harkokin kasuwanci.
Haka kuma Harris ta soki Trump da janyo rashin akin yi a Amurka a lokacin yana shugaban kasa daga 2017 zuwa 2021.
Sannan shi kuma ya soke ta a kan yawan tashin farashin kaya da ayyuka da ya ce an rika samu a lokacin mulkin Biden, kodayake ya rika kara gishiri a kan yadda aka samu karuwar farashin
Sannan kuma nan da nan ya karkata a kan babban batun da ya fi sanyawa a gaba na shige da fice, inda ya yi ikirari ba tare da wata sheda ba cewa bakin haure sun rika shiga Amurka daga iyakarta ta kudu da Medico.
‘Yar takarar ta Democrat ta gabatar da jawabi mai tsawo na suka a kan ‘yancin zubar da cikin da ake magana kan yadda take ganin an danne wa mata ‘yancinsu na samun kulawar gaggawa a harkar lafiya, da kuma yadda matan suka rasa damar zubar da ciki saboda dokoki na jihohi da suka samu gindin zama tun bayan da kotun kolin kasar ta kawar da damar da jihohi ke da ita a kan hakan a 2022.
Hukuncin da ta danganta da alkalai uku na kotun da Trump ya nada.
A kan manufofin waje Mista Trump ya ki ya masa cewa ko yana ganin ya kamata Ukraine ta yi nasara a yaki da Rasha, yayin da ya zargi Harris da tsanar Isra’ila.
A kan batun na Ukraine Harris tana nuna goyon baya ne ga wadanda ta kira kawayen Amurka, yayin da ta jadda ‘yancin Isra’ila na kare kanta da tabbatar da tsaronta, to amma tana ganin hanyar lafiya ita ce samar da kasashe biyu na Isra’ila da kuma Falasdinawa da ta ce sun cancanci samun tasu kasar cikin ‘yanci da walwala.
Mis Hariis ta soki Trump a kan samun sa da kotu ta yi da laifi a kan shari’arsa ta bayar da kudi na toshiyar baki ga fitaccciyar mai fim din batsa da ya yi mu’amulla da ita da sauran laifuka da aka same shi da su.
Trump ya musanta aikata wani laifi a nan inda ya sake zargin Harris da jam’iyyarta ta Democrat da kulla masa sharri a kan dukkanin wadannan laifuka ba tare da sheda ba.
Haka kuma Trump ya sake ikirarinsa na cewa zaben 2020 ya fadi ne saboda magudi da ya ce an yi masa.
Yanzu dai mako takwas ya rage a yi zaben.