• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Trump Na Son Karbe Ikon Gaza Domin Sauya Wa Falasdinawa Matsuguni

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
9 months ago
Gaza

Donald Trump ya firgita Falasdinawa kan shawarwarinsa game da makomar zirin Gaza, saboda ya ce Amurka za ta kwace iko da zirin tare sauya fasalinsa.

Wannan ne sauyi mafi girma game da manufofin Amurka kan yankin gabas ta tsakiya cikin gomman shekaru.

  • Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
  • A Rungumi Hakuri A Zaman Aure ‘Yan’uwa Mata

Trump ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a fadar White House tare da firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

“Amurka za ta karbi ikon zirin Gaza kuma za mu mallake zirin kuma mu dauki alhalin kwance nakiyoyin da aka dąsa sannan kuma gyara wuraren da aka lalata,” in ji Trump.

Nan da nan firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya nuna jin dadinsa ga kalaman na Mr Trump, inda ya ce hakan zai canza tarihi.

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

Netanyahu ya ce “Ina kara maimaitawa, muradinmu uku ne kuma na uku shi ne tabbatar da cewa zirin Gaza bai kara zama barazana ga Isra’ila ba.”

Shugaban Amurkar ya kuma bayyana abin da yake tunani game da makomar gabar yamma da kogin Jordan, inda ya ce yana tunanin nuna goyon bayansa ga shirin Isra’ila na kwace iko da gabar yamma din.

Netanyahu dai shi ne shugaban wata kasa na farko da ya kai ziyara fadar White House tun da Trump ya koma kan karagar mulki a karo na biyu.

Abin da Trump ya fada kan kwace Gaza

“Amurka za ta karbe zirrin Gaza, kuma za mu yi abin da ya dace. Za mu mallake shi kuma za mu dau nauyin tsaftace zirrin da lalata duk wasu abubuwan fashewa masu hadari da bama-bamai da ba su fashe ba, da sauran makamai.

“Za mu daidaita komai da kau da gidajen da aka ruguza. Za mu share birnin da samar da ci gaba na tattalin arziki da zai samar da ayyuka mara iyaka da gidaje ga mutanen yankin.

“Za mu yi aiki na gaskiya. Za mu yi abubuwa na daban. Babu koma wa baya. Koma wa baya na nufin a sake fadawa gidan jiya irin yanayin da ake ciki shekaru 100 baya.”

Bayan wadannan kalamai, An yi wa Trump tambayar cewa wane irin iko yake da shi na raba mutane miliyan 1.8 da Gaza.

Martaninsa: “Na hango mun mallake wannan wuri, sannan na hango yadda hakan zai tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki na gabas ta tsakiya, babu mamaki baki daya Gabas Ta Tsakiya ma, kuma duk wanda na yi magana da shi, ya fahimci hakan ne mafita.

“Duk mutanen da na tattauna da su, sun nuna goyon-baya da wannan shawara ta Amurka na mallake zirrin, samar da cigaba da ayyuka ga dubbai, tsari ne da ba a taba ganin irinsa ba.”

Me Trump ya ce kan sake tsugunar da al’ummar da ke Gaza a yanzu?

Kafin a shiga taron manema labarai, Trump ya tattauna da Netanyahu a gaban manema labarai a Fadar White House, inda ya yi wadannan kalamai:

“Idan aka yi waiwaye, kullum mutuwa ake yi. Abu ne da an shafe shekaru yana faruwa, kullum mutuwa. Idan muka samu wuri mai kyau da za mu tsugunar da mutanen na dindindin a gidaje masu kyau, inda za su yi rayuwa cikin farin ciki, babu batun harbi ko kashe su, babu batun kashe su da wuka kamar abin da ake gani a Gaza…

“Ina ganin babu laifi sake tsugunar da su, kuma ina ganin za mu cimma hakan a yankunan da shugabannin ke cewa A’a.”

Me Trump ya ke cewa kan mafita da yanayin da Gaza zai kasance?

A karshen taron manema labaran, Trump ya ambato muradansa kan yanayin da Gaza zai kasance nan gaba:

“Har na hango mutane na rayuwa a can, mutane daga sassa na duniya. Ina ganin za mu mayar da zirrin wani yanki da duniya ta jima ba ta gani ba. Gaza wuri ne da ke da dimbin albarkatu.

“Ina ganin duk duniya – wakilai daga ko ina a duniya – za su kasance a can, su ma Falasdinawa za su zauna acan, mutane da dama za su zauna a can…

“Dole mu koyi da abubuwa daga tarihi, ba za mu bari tarihi ya ci gaba da maimaita kansa ba. Muna da damar yin abubuwa na daban.

“Za mu tabbatar mun yi abin da zai kai kololuwa a duniya, zai kayyatar da mutane, Falasdinawa musamman da ake magana a kansu. Duk da dai suna nuna adawa, ina da yakinin cewa Sarkin Jordan da kuma Kasar Masar za su bude mana zuciyarsu da bamu irin yankin da muke so, saboda tabbatuwar burinmu, mutane su yi rayuwa cikin hadin-kai da annushuwa.”

Hamas ta yi tir da Trump

Jim kadan bayan Trump ya kammalan wadannan jawabai na sa ga ‘yan jarida – daya daga cikin jagororin Hamas, Sami Abu Zuhuri ya ce wadannan shawarwari na Trump shirme ya ke yi kuma sun yi tir da hakan.

Ya bayyana matakin da shirin haifar da hargitsi da rashin kwanciyar hankali a yankin.

“Duk irin wadannan shawarwari yunkuri ne na ingiza rikici,” a cewarsa, kamar yadda kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rawaito.

Abu Zuhri ya kuma yi martani kan batun da Trump ke yi cewa a sake wa ‘yan Gaza matsugunai a kasashe da ke kurkusa, yana cewa wannan wani lamari ne na sake kunna wutar sabon rikici da tashin hankali a gabas ta tsakiya”.

“Mutanenmu da ke zirrin Gaza ba su yarda da wannan shiri ba. Abin da ake bukata shi ne kawo karshen mamaya da musgunawa mutane, ba raba su da yankinsu,” kamar yadda ya fadawa ‘yan jarida.

Kalaman Trump na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kokari na shiga tsakani domin kawo karshen yakin Isra’ila da Hamas, a mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni.

Kasashen Larabawa sun bijire

Saudiyya ta mayar da martani cikin gaggawa kan kudurin Trump na shirin kwace iko da zirin Gaza, inda ta yi watsi da duk wani yunkuri na raba Falasdinawa da kasarsu.

Saudiyyar ta ce ba za ta kulla wata alaka da Isra’ila ba har sai an samar da kasar Falasdinu.

Kasashen Masar da Jordan suma sun bayyana rashin amincewarsu da yunkurin na Trump na tsugunnar da Falasdinawa a kasashensu.

A wata sanarwar hadin-gwiwa, shugabannin kasashe daga Gabas Ta Tsakiya da kungiyoyi sun yi gargadi abin da ka iya biyo bayan wannan shiri, sannan sun ce babu wanda zai aminta da duk wani yunkuri na share wata al’umma ko rabata da asalinta.

Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya ce ‘yan Gaza na son komawa gidajensu da sake gina yankin, saboda nan ne “asalinsu kuma suna son rayuwa a inda yake nasu.”

“Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata shugabanni su ke mutunta muradai da fatan Falasdinawa,” a cewarsa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Manyan Labarai

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Next Post
Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin

Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.