Shugaban Amurka, Donald Trump, ya aike wa BBC wasiƙar gargaɗi tare da barazanar shigar da kara ta hanyar neman dala biliyan daya ($1bn) kan wani rahoto ds ta shafi wasu jawabansa da ya yi kafin magoya bayansa su afka majalisar dokokin Amurka a watan Janairun 2021.
Rahoton da BBC ta shirya ya haɗa wasu jawabansa biyu waje ɗaya, abin da shugaban BBC ya bayyana a matsayin kuskure.
- Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika
- Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
Lamarin ya kai ga shugaban BBC da shugabar sashen labarai ajiye muƙamansu, bayan musanta cewa BBC tana nuna son kai a rahotanninta.
Lauyoyin Trump sun bai wa BBC wa’adin ranar Juma’a don ta janye rahoton, tare da bayar da haƙuri a fili, kuma ta biya diyya, ko kuma a ɗauki matakin shari’a.
BBC ta ce tana duba wasiƙar da lauyoyin Trump suka aike mata.
Tawagar lauyoyin Trump ta ce an ɓata masa suna da mutunci, inda ta bayyana cewa BBC ta yi hakan ne don siyasa.
Trump ya taɓa shigar da ƙorafe-ƙorafe makamantan wannan a kan wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da ABC, CBS, da The New York Times, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya a kansa.














