Tsohon Sanata, Shehu Sani, ya bayyana sabon shugaban Amurka, Donald Trump, a matsayin “mai tayar da ƙura” wanda ya ce zai fuskanci manyan ƙalubale daga gida da waje.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, sa’o’i kaɗan kafin rantsar da Trump a matsayin shugaban Amurka na 47, Sani ya yi gargaɗin cewa mulkin Trump zai kawo ƙalubale a duniya.
- Trump Ya Sake Ɗarewa Kan Mulkin Amurka, Sabbin Ƙudirorinsa Sun Bar Baya Da Ƙura
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Samun Ingantar Tattalin Arziki
Ya ce, “A yau Mista Trump zai karɓi mulkin shugabancin Amurka.
“A matsayinsa na mai tayar da ƙura ya ɗauki madafan iko, kuma hakan zai zama babban ƙalubale ga duniya.
“Zai kasance mai kishin Amurka da ‘yan kasuwa da ke kan gaba wajen ƙalubalantar duniya.”
Sani ya nuna cewa Trump na iya sauya dangantakar Amurka da ƙungiyoyi da ƙasashe a duniya.
Ya ce, “Zai yanke hulɗa ko kuma canza tsarin hulɗa da MDD, EU, NATO, da kuma dangantakar Amurka da sauran ƙasashe.
“Za a ji tsoronsa ba soyayya ba, kuma zai fuskanci tirjiya daga abokan hulɗa da ma abokan gaba.”
Ya kuma ja hankalin Afrika game da tasirin mulkin Trump, yana mai cewa, “Afrika kada ta yi tsammanin wani abu mai yawa daga Trump, duk da cewa Biden ma bai yi wani abin a-zo-a-gani ba.
“Duniya bai kamata ta yarda ko ta yasar da ƙimarta na ɗabi’un ɗan Adam na duniya ba.”
Sani ya ƙare da cewa yunƙurin Trump na sake fasalta tsarin duniya zai haifar da rashin jin daɗi da kuma tirjiya a ko ina cikin duniya.