Shugaban Amurka Donald Trump zai shirya wata liyafa ta musamman a ranar Alhamis ga manyan masu zuba jari a kuɗin cryptocurrency nasa na meme coin mai suna $TRUMP.
Taron za a yi shi a wurin wasan golf na Trump dake Virginia, inda manyan masu sayan jarin $TRUMP 220 za su yi cin abinci tare da shugaban, yayin da manyan masu zuba jari 25 za su kuma yi wata ganawar sirri da kuma rangadin Fadar White House.
- Gwamnatin Trump Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadanci A Afrika
- Zan Ba Ku $1,000 Kyauta In Zaku Koma Garuruwanku – Trump Ga Baƙin Haure
Wasu ‘yan siyasa kamar Sanata Chris Murphy sun yi kakkausar suka kan taron, yana mai zargin cewa hanyar ce ta siyan damar shiga jikin shugaban ƙasa, musamman ga masu hannu da shuni na ƙasashen waje.
Duk da haka, Fadar White House ta yi tir da waɗannan zarge-zarge, ta bayyana cewa Trump ya bar kasuwancinsa mai albarka domin hidimar jama’a.
Taron ya zo ne a lokacin da Majalisar Dattijai ke gabatar da dokar GENIUS Act don tsara kasuwancin cryptocurrency, wanda ke nuna ƙaruwar sha’awar shugaba Trump a fannin kuɗi na zamani dijital.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp